A wani mataki na nuna kara kusanci tsakanin kasashen Somaliya da Habasha, shugaban kasar Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci Somaliya.
A Shekara guda da ta wuce, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna.
Bayan shafe shekara guda ana zaman dar-dar, a watan Disambar da ya gabata ne a kasar Turkiya, kasashen biyu suka sake kulla huldar jakadanci ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar Ankara.
Shugaban kasar Somaliya Hassan Cheikh Mohamoud ya gabatar a matsayin “mahimmin mataki” na daidaita huldar dake tsakanin kasashen biyu.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar da yammacin jiya Alhamis, an bayyana cewa: Habasha da Somaliya kasashe ne masu dogaro da juna da makoma guda da kuma ra’ayi daya na tabbatar da zaman lafiya da wadata a yankin.
An tattauna dangantakar diflomasiyya, yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin, da kuma batutuwan tattalin arziki, musamman sha’awar Habasha na samun damar shiga teku.
A halin da ake ciki dai mahukuntan Somaliyan sun dauki matakin saukaka jigilar kayayyaki daga Habasha zuwa tashar jiragen ruwa na Somaliya, musamman na Berbera dake yankin Somaliland.