Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikata biyar bayan da suka nuna rashin amincewa da kwangilar da kamfanin ya kulla da sojojin Isra’ila.
A rahoton cibiyar yada labarai ta Falasdinu, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, sanye da riguna masu dauke da taken nuna adawa da amfani da fasahar kamfanin wajen kai wa Falasdinawa hari.
Matakin ya zo ne bayan da aka buga wani rahoto da ke nuna cewa an yi amfani da bayanan sirri na wucin gadi da na’urar tantance gajimare na Microsoft wajen ayyukan sojojin Isra’ila.
Bayan wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya yi a baya-bayan nan, ya bayyana cewa kamfanonin fasahar kere-kere na Amurka sun taimaka wa Isra’ila wajen kara yawan laifuka da kashe-kashe a Gaza da Lebanon ta hanyar samar da kayayyakin leken asiri ga gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta bayar da wani rahoto da ke cewa, Microsoft ya karfafa alakarsa da sojojin Isra’ila tare da ba su tallafin fasaha a yakin Gaza.
Jaridar Guardian ta kara da cewa dogaron da sojojin Isra’ila suka yi kan fasahar Microsoft ya karu matuka a lokacin yakin Gaza, kuma sun yi amfani da hakan wajen aiwatar da kashe-kashe kan Falastinawan Gaza.