Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba da takun tsakar dake wakana (…) Aljeriya ba ta dauki wani mataki ba, kuma ta bar bangaren Faransa da ta matakin da ya dace.
Ita dai Faransa ta yi barazana a ranar Laraba cewa za ta binciki yarjejeniyoyin da ke saukaka yanayin zama, shige da fice da kuma aiki ga ‘yan Aljeriya, dangane da koma bayan da ake samu na tashe-tashen hankula sakamakon wani hari da aka kai a Mulhouse.
Firaministan faransa, François Bayou ya ce kin karbar ‘yan kasar Aljeriya da aka aka kora daga Faransa ba abu ne da ba za a amince da shi ba, wanda a saboda haka ya baiwa Algiers wa’adin makonni 6 domin nuna aniyar ta na yin hadin gwiwa sosai a kan batutuwan da suka shafi bakin haure, inda ya yi barazanar duba yarjejeniyar 1968 dake tsakanin kasashen biyu.
Kasashen faransa da Aljeriya sun shiga tsakun tsaka matuka a baya baya nan musamman kan batun yankin yammacin sahara na ‘yan Polisario da Aljeriya ke goyan baya, wanda faransa ta amince da ikon shi ga kasar Morocco.
Ko a makon nan majalisar al’ummar Aljeriya, kwatankwacin majalisar dattijai ta kasar, ta sanar da cewa ta “dakatar da hulda da majalisar dattawan Faransa, domin nuna adawa da ziyarar da shugabanta Gérard Larcher ya kai a ranakun Litinin da Talata a yankin yammacin Sahara.