Iran Ta Yi Tir Da Kakkausar Murya Kan Barazanar Soji Da Isra’ila Ke Yi Mata

Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin

Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin tsaron kasar a matsayin rashin hankali da wauta.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana a jiya Alhamis yayin da jami’an Isra’ila ke ci gaba da yi wa Iran barazanar daukar matakin soji, kasashen yamma na ci gaba da zargin kasar da kara karfin tsaronta.

M. Baqaei ya yi nuni da cewa, yankin yammacin Asiya na fama da wata mamaya da ta dade wacce kamu ta wuce gona da iri da rashin bin doka da oda.

Don haka ya kara da cewa, wajibi ne kawai Iran ta kara karfin tsaronta.

Kalaman nasa sun zo ne bayan ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce ana bukatar daukar matakin soji don dakatar da shirin nukiliyar Iran.

A cikin shekarun da suka gabata, kasashen Yamma sun soki ayyukan Iran a kan shirin nukiliyarta, jirage marasa matuka, tsaron sararin samaniyarta, da kuma shirye-shiryen makamai masu linzaminta, suna masu neman Tehran ta dakatar da su.

Iran ta sha nanata cewa ci gaban da take samu na soji ne kawai don kara kaimi ga kasar kan barazanar abokan gaba, musamman Isra’ila da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments