7 Oktoba : Sojin Isra’ila Sun Amince Da “Cikakkiyar Gazawa” A Harin Hamas

Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba,

Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar.

A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, jami’an sojin sun amince da cewa sun kasa cika aikinsu a ranar da Hamas ta kai wa Isra’ila hari.

Wani jami’in soji ya shaidawa gidan radiyon RFI cewa sojojin sun “kasa cika aikinsu na kare fararen hula Isra’ila” a harin na ranar 7 ga Oktoba, 2023, yayin da aka fitar da babban sakamakon binciken.

Ya kara da cewa “Fararen hula da dama ne suka mutu a wannan rana kuma suna mamaki ga inda sojojin Isra’ila suke a yayin harin.”

Sojojin sun amince da cewa sun yi kuskure ne game da karfin soja na Hamas, in ji shi.

Baya ga gazawar sojojin Isra’ila, binciken ya yi cikakken bayani kan harin na Hamas da ya yi sanadin mutuwar mutane 1,218 a bangaren Isra’ila, galibi fararen hula, a cewar alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar bisa bayanan hukuma na Isra’ila.

A cewar wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya-bayan nan, kashi 70 cikin 100 na ‘yan Isra’ila suna neman a kafa wata hukumar bincike mai zaman kanta don ba da haske kan wadannan abubuwan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments