Kungiyar Hamas Ta Dakatar Da Tattaunawa Da HKI Har Zuwa Sakin Fursinoni Falasdinawa

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka […]
Iran A Karon Farko Ta Gwada Aiki Da Sabbin Jiragen Yakin Da Ta Kera A Cikin Atisayen Zulfikar da Ke Gudana A Halin Yanzu

Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin […]
IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta […]
Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar

Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen […]
An Sanya Sayyid Safiyyuddeen Shahidi A Makwancinsa Ta Na Karshe A kudancin kasar

A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka […]
Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi

Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah. A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin […]
Al-Khazali: ‘Yan gwagwarmaya a Iraki za su gaba da bin tafarkin Sayyid Nasrallah

Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai […]
Iran na da niyyar kara karfafa alakarta da kasashen Afirka

Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a […]
Kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun kara zurfafa alakar da ke tsakanin juna

A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da […]
Pezeshkian: Hizbollah tana nan a raye a kan tafarkin gwagwarmaya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana […]
Hamas ta yaba da irin goyon bayan da Sayyed Nasrallah ya baiwa Falasdinu

Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya […]
Tawagar Iran a Beirut ta gana da shugabannin Lebanon

Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun. Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin […]
Kungiyar RSF da kawayenta na shirin kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan

Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta […]