Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya.
A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da mamaya.
Shugaban kasar Iran ya jinjinawa shahidan gwagwarmaya da suka hada da Sayyed Hassan Nasrallah, tare da tunawa da sadaukarwa ta dukkanin mujahidan da suka yi shahada suka yi a yayin karawa da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Bazeshkian ya yi nuni da cewa: “Masu da’awar cewa gwagwarmaya za ta ruguje tare da shahadar Sayyid Nasrallah, a maimakon haka, Hizbullah ta ci gaba da kara jajircewa ne a kan matsayinta na yaki da zalunci da mamaya ta sahyuniyawa.