Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran).
Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba.
Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran) na cikin ajandar gwamnati ta 14 a Iran.
Aref ya jaddada cewa, bunkasa cikakken hadin gwiwa tare da nahiyar Afirka a fannin tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu, da sauran bangarori daban-daban, shi ne fifiko ga Iran, yana mai cewa: Idan aka yi la’akari da irin karfin da bangarorin biyu suke da shi, yin hadin gwiwa da tattara dukkan albarkatu da karfinsu, to za su iya ba da gudummawa sosai ga ci gaban dangantaka da hidima ga jama’arsu.