Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana.
Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta.
Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa.
“Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar Falastinu daga mamayar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawan sahyuniya, in ji shi.
A cewar Hani Khater, shugaban ofishin yada labarai na Al-Ahed na kasar Iraki a ofishin Tehran, kimanin ‘yan kasar Iraki dubu 200 ne suka halarci jana’izar Sayyed Nasrallah a jiya Lahadi a birnin Beirut.
Sannan kuma Ya yi nuni da cewa, akidar Sayyed Nasrallah za ta ci gaba da dawwama a duk fadin yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.