Tawagar Iran a Beirut ta gana da shugabannin Lebanon

Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar

Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun.

Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, sannan ta ci gaba da tattaunawa da sauran jami’ai da suka hada da firaministan kasar Labanon Nawaf Salam.

Ghalibaf da sauran jami’ai sun tafi kasar Lebanon a safiyar Lahadi don halartar jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah, da kuma magajinsa  Sayyed Hashem Safieddine, wadanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kashe su a karshen shekarar da ta gabata.

Da yake zantawa da manema labarai gabanin tafiyar tasa, Ghalibaf ya bayyana jana’izar a matsayin wani lokaci mai ma’ana ga kungiyar gwagwarmaya, duniyar musulmi, da kuma al’ummar Lebanon.

A lokacin da ya isa birnin Beirut babban jami’in na Iran ya bayyana Nasrallah a matsayin wani mutum mai babban matsayi kuma abin alfahari ga duniyar musulmi, yana mai jaddada abin da ya bari a matsayin wata alama ta tsayin daka a kan yakin kisan kare dangi na “Isra’ila” a Gaza.

Ghalibaf ya kara da cewa, duk da shahadarsu, amma Hizbullah da al’ummar Lebanon na alfahari da wadannan gwaraza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments