A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka a yankin da dama sun halarci jana’izar.
Mutane daga kasashen duniya da dama wadanda suka halarci jana’izar a jiya Lahadi a Beirt sun halarci jana’izar Sayyid shahid Hashim safiyyudeen a yau a kudancin kasar ta Lebanon.