Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin saman yaki samfurin Yak-130 a cikin atisayen. Inda suka tabbatar da ingancinsa.
Ana gudanar da atisayen Zulfikar 1403 ne a yankin Tekun Omman da kuma wani bangare na yankin Tekun farasa daga kudancin kasar Iran.
Bugediya Janar Alireza Sheikh kakakin atisayen ya fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa wannan bangare kadan ne daga atisayen, amma a yau sun gwada karfi da ingancin samfurin jiragen yaki yak-130 ne a karon farko kuma sun kara tabbatar da ingancisu.
Janar Sheikh ya kara da cewa wannan hotunan bidiyo da kuka ganin bangare ne na inda jirgin ya gwada korewarsa na kakkabo wani jirgi wanda ake sarrafashi daga nesa na makiya tare da amfani da garkuwan makami mai linzami samfurin MiG-29. Sannan an ga yadda ya sami nasarar kakkabo shi.