Kungiyar RSF da kawayenta na shirin kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan

Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin

Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba.

Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin  Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga kowane al’adu, kabila, addini, ko yanki ba.

Gwamnatin da aka gabatar na shirin magance gibin ayyuka a yankunan RSF a cewar Alaa El-Din Nuqd, wanda ya jaddada cewa “An katse al’ummar wadannan yankuna daga muhimman ayyuka kamar sabbin takardun kudi da sojoji suka fitar, sarrafa fasfo, da sabunta takardu,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto.

Mai magana da yawun rundunar RSF Najm al-Din Drisa ya ce za a iya kafa sabuwar gwamnati nan da wata guda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments