Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah.
A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta shiga wani sabon yanayi na kara tabbatar wa duniya da cewa ita bata bin dokokin kasa da kasa.
Baghaei ya ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tarwatsa dubban daruruwan ‘yan kasar Lebanon da wasu da suka taru domin nuna girmamawa ga jarumtansu, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da mataimakinsa da suka nada Sayyed Hashem Safieddine.
Baghaei ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan mataki na rashin da’a, da rashin girmamam dokokin duniya da Isra’ila ta nuna a jiya a lokacin janazar Sayyid Hassan Nasrullah a Beirut.