Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar

Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane

Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi.

Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza  a jiya Lahadi. Ya kara da cewa gwamnatin kasar Iraki ta maida hankali sosai kan yan ta’adda ta Daesh ne saboda yankunan hamadan mai yawa da ke da tsakanin kasashen biyu. Ta inda mai yuwa wasu daddaikun yayan kungiyar su sulale su shiga kasar ta Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments