Kungiyar Hamas Ta Dakatar Da Tattaunawa Da HKI Har Zuwa Sakin Fursinoni Falasdinawa

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce kungiyar ta saki fursinoni yahudawa  6, kuma take fatan HKI za ta saki falasdinawa 620 kamar yadda yake cikin yarjeniyar tsagaita wuta, amma ta ki yin hakan, da dalilin cewa wai kungiyar Hamas ta wulakanta daya daga cikin fursinoni 6 da ta saka.

Jami’in na Hamas ya ce tawagar tattaunawar Hamas ba za ta gana da tawagar HKI don tattauna ci gaban da ke cikin yarjeniyar tsagaita wutar ba, har zuwa lokacinda HKI ta sake wadannan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments