Pezeshkian: Ba za mu sunkuyar da kawunanmu gaban wata kasa ta duniya

Zababben shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa ba zai durkusa a gaban wani mai mulki a duniya ba, yana mai jaddada cewa kalaman

Zababben shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa ba zai durkusa a gaban wani mai mulki a duniya ba, yana mai jaddada cewa kalaman da ya yi a baya-bayan nan ba take  ba ne, Magana ce da ya yi imani da ita.

Ya ci gaba da cewa: Al’ummar Iran sun dora mini babban nauyi kuma mai girma, ya kara da cewa: “Ba tare da goyon baya da taimakon al’umma ba, kuma ba tare da manyan mutane, masana da ma’aikata a bangarorin samar da kayayyaki, da masana’antu, da bangaren noma sauransu, da kuma taimakon malaman addini ba, ba zan iya cimma komai ba.”

A jawabin da ya yi a jiya Alhamis ga mambobin yakin neman zabensa a birnin Tehran, Pezeshkian ya yi alkawarin yin gaskiya ga al’ummar Iran da kuma cika alkawuran da ya dauka.

A jawabinsa na farko ga al’ummar Iran bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa, Pezeshkian ya bayyana cewa kuri’un jama’a na nufin wani nauyi da kuma alkawari a wuyansa,” yana mai jaddada cewa ya zo ne domin ya zama mai hidima ga al’ummar Iran, da kuma ci gaba da bunkasar kasar,  yana mai jaddada cewa bai yi alkawari na karya ba, kuma bai yi alkawarin wani abu da ba zai iya ba.

Pezeshkian ya jaddada bukatar bude wani sabon shafi da hada kan dukkanin bangarori na kasar Iran, tare da fatan majalisar dokokin kasar za ta yi abin da ya dace ga gwamnati mai zuwa, domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a kasar.

A game da manufofin ketare, ya jaddada cewa goyon bayan da Iran take ba wa dakarun gwagwarmaya yana kawo daidaito, yana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana daukar goyon bayan al’ummar Palastinu da gwagwarmayar da suke yi, da kuma taimaka musu wajen yaki da mamaya da zaluncin da gwamnatin wariya ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi musu a matsayin wani aiki na wajibi na addinin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments