Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A Gaza Yayin Da Ake Ci Gaba Da Tattaunawar Neman Tsagaita

Rahotanni daga Gaza na cewa an gwabza kazamin fada da ruwan bama-bamai a Zirin da wasu yankunan Falasdinawa a yau Juma’a yayin da masu shiga

Rahotanni daga Gaza na cewa an gwabza kazamin fada da ruwan bama-bamai a Zirin da wasu yankunan Falasdinawa a yau Juma’a yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da kokarin dakatar da yakin da ya shiga cikin wata na goma.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a taron Ƙungiyar Tsaro ta NATO a birnin Washington jiya Alhamis cewa jami’an diflomasiyyar Amurka, duk da matsalolin da ake fuskanta, suna samun “ci gaba” tare da masu shiga tsakani na kasa da kasa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da jaddada cewa “lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan yaki”.

Kafofin yada labarai masu alaka da Hamas, sun ce sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 32, tana mai cewa “an kai wadanda suka mutun, wadanda akasarinsu yara da mata ne zuwa asibitoci cikin dare, saboda kisan kiyashin da ake ci gaba da yi”.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana kuma gwabza fada a yankin Rafah da ke kudancin kasar, a hare-hare ta sama”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments