Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa: A yau Netanyahu, Ben Guerr da Smotrich, su ne ke fafutukar kare muradun kansu da tabbatar da ci gaba da kasancewa kan mulki ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da kashe mata da kananan yara, da rusa gidaje da cibiyoyi da asibitoci da makarantu.
Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana hakan en a wani jawabi da ya gabatar birnin Beirut, inda ya bayyana cewa, mayakan ‘yan gwagwarmaya na ci gaba da samun galaba a kan makiya domin kasancewa a sahun gaba na yakin guguwar Al-Aqsa, ya ce tun daga ranar da Isra’ila ta kaddamar da hari kan al’ummar Gaza, Hizbullah ta shiga cikin yakin, domin taimakon al’ummar Gaza.
Ya kara da cewa: “Mun sami damar mamaye wani bangare mai yawa na karfin makiya da sojojinsu da kuma nisantar da makiya daga cimma burinsu a yakin Gaza.” Mun jaddada cewa arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye tana da alaka da Gaza, kuma yahudawan da ke wannan basu ga kwanciyar hankali ba, har sai gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo karshen kisan kiyashi a Gaza.
Ya ce: Kisan mata da kananan yara da rusa makarantu da masallatai da kasuwanni gami da asibitoci ba nasara c eta yaki ba, wannan aiki ne na matsorata, wanda kuam shi ne abin da sojojin Isra’ila suke yi a gaza, maimakon babban abin da suka ambata cewa shi ne manufarsu wato kawo karshen kungiyar Hamas, da kuma kwato yahudawa da ake tsare da sua Gaza da karfin tuwo, wanda babu ko daya dagga cikin wadannana bubuwan biyu da ya tabbata.