Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da mummunan yakin Isra’ila a Gaza, yana mai tir da “sabon misali mai ban tsoro na ukubar da fararen hula suke sha”, a zirin a cewar kakakinsa.
“Wannan wani misali ne mai ban tsoro na ukubar da Falasdinawa fararen hula, maza, mata da yara ke sha a kokarin tsira da rayukasu, a fadin Gaza inji,” Stéphane Dujarric ga manema labarai,.
A nasa bangare Josep Borrell, shugaban diflomasiyyar Turai, ya nuna takaici kan harin yakuma bukaci a yi “bincike mai zaman kansa”.
A jiya ne Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce Isra’ila ta kai hari kan daya daga cikin makarantunta a Gaza “ba tare da yin gargadi ba” ga dubban masu neman mafaka a wajen.