‘Yan gwagwarmaya a Yaman da Iraki sun kaddamar da farmakin hadin gwiwa kan Isra’ila

Dakarun kasar Yemen da dakarun gwagwarmaya na kasar Iraki sun kaddamar da sabbin hare-hare na hadin gwiwa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, domin mayar da

Dakarun kasar Yemen da dakarun gwagwarmaya na kasar Iraki sun kaddamar da sabbin hare-hare na hadin gwiwa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, domin mayar da martani  kan yakin kisan kare dangi da take kan Falasdinawa a Gaza.

Kakakin Rundunar Sojin kasar Yaman Brigadier General Yahya Saree ya fada a jiya Alhamis cewa, dakarun hadin gwiwa na Yaman da Iraki, sun kaddamar da hare-hare kan wasu jiragen ruwa guda uku a tekun Maliya da kuma Tekun Arabian Sea, da suke dauke da kayayyakin soji a tashar jiragen ruwan Isra’ila da ke Haifa.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Iraki a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa: A ci gaba da bin tafarki na tinkarar zaluncin yahudawan Isra’ila, da kuma nuna cikakken goyon bayanmu ga al’ummar Palastinu, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da ‘yan ta’adda suke  yi wa fararen hula mata da kananan yara, da kuma Tsofaffi a Gaza, dakarun gwagwarmayar musulunci a Iraki sun gudanar da ayyukan soji biyu na hadin gwiwa tare da Sojojin Yaman a tashar Haifa ta hanyar amfani da jirage marasa matuka.”

Sanarwar ta kara da cewa, dakarun gwagwarmaya a Iraki suna kan bakansu na ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka a dukkanin maboyar makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments