Search
Close this search box.

Putin: Iran ta cika alkawuran da ta dauka kan yarjejeniyar nukiliya

A gefen taron na St.Petersburg, Putin ya kare matakin Iran na yin riko da alkawurra na yarjeneiyar nukiliya karkashin hukumar ta IAEA, yana mai nuni

A gefen taron na St.Petersburg, Putin ya kare matakin Iran na yin riko da alkawurra na yarjeneiyar nukiliya karkashin hukumar ta IAEA, yana mai nuni da yadda kasashen Rasha da Iran ke ci gaba da habaka hadin gwiwa a tsakaninsu a wani mataki na mayar da martani ga zagon kasar da kasashen yammacin duniya ke yi kan shirin Iran na nukiliya na zaman lafiya.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana hakan ne a gaban ‘yan jaridu na kasashen waje a gefen taron dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na St.

Dangane da haka, Vladimir Putin, yayin da yake mayar da martani ga tambayar Ali Naderi, shugaban kamfanin dillancin labarai na “IRNA”, a gefen taron na St. dangane da ci gaban dangantakar dake tsakanin Tehran da Moscow, Putin ya bayyana cewa, an nasarori masu tarin yawa a wannan fage tsakanin Rasha da Iran.

A wani bangare na amsar tambayar da shugaban kamfanin dillancin labaran IRNA da ya yi kan batun kare hakkin Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, shugaban na Rasha ya ce: A ra’ayinmu, Iran ta cika  alkawuran da suka rataya a wuyanta na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, kuma ba ta keta haddi ba.

Vladimir Putin ya ce; abin takaici ne yadda wasu bangarori kasashen yammacin turai da ke cikin yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, suke yin amfani da hakan a matsayin makami na siyasa, tare da fito da salon siyasarsu ta munafunci da harshen damo a fili.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments