Spain ta shiga cikin karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar gaban kotun kasa da kasa kan “Isra’ila” game da laifukan kisan kare dangi da take aikatawa a yakin da take ci gaba da yi a zirin Gaza tsawon watanni 8.
Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albarez ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa za ta shiga cikin karar kisan kare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar gaban kotun kasa da kasa kan ayyukan yakin Isra’ila a zirin Gaza da ke Falasdinu.
A kan haka, Spain ta zama kasa ta biyu a Turai da ta shiga cikin lamarin, wanda Ireland a baya ta shiga, baya ga Chile da Mexico.
A nata bangaren, kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi marhabin da sanarwar da kasar Spain ta fitar kan shiga wannan shari’a, tana mai jaddada cewa matakin na kara karfafa adalcin kasa da kasa wajen gurfanar da ‘yan mamaya da ke aikata munanan laifuka na kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi kira ga kasashen duniya da su shiga cikin karar da aka shigar kan gwamnatin yahudawan Sahyuniya, da ke ci gaba da yin kisan kiyashi da Gaza, ba tare da yin aiki da umarnin kotun duniya ba.
Kasar Spain ta kuma dauki mataki kan batun amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken ‘yancin cin gashin kanta, kamar yadda ta sanar a hukumance a ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata, wanda kasar Falastinu ya hada da gabar yamma da kogin Jordan da zirin Gaza, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birnin kasar.”
A watan da ya gabata, Libya da Turkiyya, su ma sun shiga karar da Afirka ta Kudu ta shigar gaban kotun duniya.