Search
Close this search box.

Sojojin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Farmaki Kan Birnin Khalil Na Falasdinu

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan yankunan kudancin birnin Khalil a shirye-shiryen ba da dama ga tsagerun yahudawan sahayoniyya na mamaye wuraren kayan

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan yankunan kudancin birnin Khalil a shirye-shiryen ba da dama ga tsagerun yahudawan sahayoniyya na mamaye wuraren kayan tarihi da suke birnin

Rahotonni sun bayyana cewa: A yau Juma’a sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan wasu yankuna da dama da suke kudancin birnin Khalil domin tabbatar da cewa tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida sun samu damar mamaye wuraren kayan tarihi tare da kwashe su domin zama mallakin yahudawan sahayoniyya.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na Wafa ya bayyana cewa: Sojojin mamayar sun kai farmakin ne kan garin Karmel dake gabashin birnin Yatta, inda suka rufe hanyoyin da ke zuwa tafkin Karmel na kayan tarihi, tare da girke ‘yan bindiga a kan rufin gidaje da dama domin harbe don bafalasdinen da ya fito domin nuna rashin amincewarsa.

Har ila yau, wasu tsagerun yahudawan sun kutsa kai cikin sansanin Tarusa da aka kaurace masa, a yammacin garin Dura, inda suka kai farmaki kan Khirbet Humsa domin gudanar da ibadun Talmud a wurin. Kamar yadda sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka hau kan rufin gidajen Falasdinawa da suke kallon waɗannan wuraren don tabbatar da aminci ga tsagerun yahudawan na sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments