Wakilan kasashe da dama da suka hada da tawagar Iran sun fice daga zaman da aka yi kan Falasdinu a birnin Geneva na kasar Switzerland a lokacin da wakilin Isra’ila ya fara jawabi.
Hakan dai ya faru ne a yayin taro na 112 na kungiyar kwadago ta kasa da kasa, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a hedkwatar MDD dake birnin Geneva.
A yayin zama na musamman kan Falasdinu, tawagar Iran da wakilan kasashe da dama sun nuna rashin amincewarsu da kasancewar wani wakilin gwamnatin Isra’ila.
tawagoginmu sun janye domin nuna adawa da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza
Jakadan iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva ya bayyana hakan ne a yayin wannan taro, yayin da yake magana kan ci gaba da kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yau cewa:
Ya kamata kungiyar kwadago ta kasa da kasa ta yi Allah wadai da wadannan laifuffukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata a zirin Gaza tare da daukar kwararan matakai na tallafawa ma’aikatan Gaza.