Search
Close this search box.

Isra’ila Ta Sake Kashe Wani Adadi Na Mata Da Kanan Yara A Yankin Nusairat Da Ke Gaza

Rahotannin daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa, jiragen yakin Isra’ila suna ci gaba da kaddamar da munan hare-harea  dukkanin sassa na yankin babu

Rahotannin daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa, jiragen yakin Isra’ila suna ci gaba da kaddamar da munan hare-harea  dukkanin sassa na yankin babu kakkautawa.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Isra’ila ta kai hari kan ɗaya daga cikin makarantunta a Gaza “ba tare da yin gargaɗi ga dubban masu fararenn hula da suka fake a wurin ba, kamar yadda shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu ta Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.

Sojojin yahudawan sun kai harin ne a kan fararen hula mata da kanan yara da suka samu mafaka a karkashin kulawar cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ta UNRWA.

“An sake kai hari kan wata makaranta ta UNRWA da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka,” in ji Lazzarini, babban darakta na hukumar ta UNRWA..

Yaƙin kisan kare dangi da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar Gaza ya shiga rana ta 245 inda Falasɗinawa akalla 36,654 suka yi shahada, kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai, sannan wasu mutum 83,309 sun jikkata, bisa rahotanni na hukumomin lafiya na yankin Zirin gaza da kuma na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments