Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza tun bayan fara kai hare-haren wuce gona da iri ya karu zuwa 36,731 da kuma jikkata 83,530
Majiyoyin kiwon lafiya na Falasdinu sun sanar a yau Juma’a cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Zirin Gaza ya kai 36,731, wadanda akasarinsu yara ne da mata, tun bayan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a ranar bakwai ga watan Oktoban bara.
Haka zalika majiyoyin sun kara da cewa: Adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 83,530 tun farkon harin, yayin da akwai dubban wadanda abin ya shafa da suke karkashin baraguzan gine-gine da kuma gawarwaki a kan tituna, saboda sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun hana jami’an ba da agaji da jami’an tsaron farin kaya isa gare su.
Yayin da wani sabon rahoto yake nuni da cewa: Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun aiwatar da kisan kiyashi har sau 8 a Zirin Gaza, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 77 tare da jikkatan wasu 221 na daban, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.