Iran: Dole ne kasashen musulmi su kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza

Ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce kamata ya yi kasashen musulmi su yi amfani da karfinsu wajen kawo karshen

Ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce kamata ya yi kasashen musulmi su yi amfani da karfinsu wajen kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza, tare da gaggauta kai kayan agaji zuwa yankin da yaki ya daidaita.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry, Bagheri Kani ya yi gargadi game da sakamakon ci gaba da cin zarafi da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kudancin birnin Rafah.

Bagheri Kani ya kuma yi ishara da alakar da ke tsakanin Tehran da Alkahira tare da jaddada muhimmancin kara yin shawarwari a tsakanin bangarorin biyu da nufin maido da hulda btsakaninsu bisa ka’idojin mutunta juna da moriyar juna.

Ya ce; Isra’ila ta killace daukacin yankin zirin Gaza, tare da katse man fetur, wutar lantarki, abinci da ruwan sha  ga Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke zaune a wurin.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Masar ya ce kawo yanzu mahukuntan kasashen biyu sun yi wata tattaunawa mai ma’ana da nufin maido da dangantaka tsakanin Masar da Iran.

Shoukry wanda kasarsa ta dade tana shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Falasdinu, ya kara da cewa a cikin watannin da suka gabata, Alkahira na kokarin dakatar da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, tare da shirya tsari na aikewa da kayan agaji zuwa yankin.

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun amince da ci gaba da tuntubar juna kan hanyoyin inganta alaka da kuma kawo karshen laifukan yakin da Isra’ila ke tafkawa kan al’ummar Palastinu a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments