Yemen:Tasha Da Tasha Wuta Da Wuta A Yaki Da Saudia

Yakin Yemen da saudiya ya shiga wata marhala ta tasha da tasha wuta da wuta. A daren jiya jumma’a ce sojojin kasar Yemen suka maida

Yakin Yemen da saudiya ya shiga wata marhala ta tasha da tasha wuta da wuta. A daren jiya jumma’a ce sojojin kasar Yemen suka maida martanin hare haren da jiragen yakin saudia suka kai a kan lardunan Hudaida, Sa’ada da kuma Makha insa suka lalata tashar jiragen ruwa ta Hudaida suka lalata tashar bada wuran lantarki a sa’ada da kuma Makha.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a daren jiya Jumma’a sojojin kasar Yemen sun kai hare haren maida martani kan tashar jiragen ruwa na Jizan da kuma cibiyar bada wutan lantarki na Shakik. Da wannan kuma an shiga wata marhala daban a yakin da kasashen biyu suke fafatawa tun watan Yulin da ya gabata.

Gwamnatin kasar Yemen ta bayyana cewa daga yanzun kuma ba zata amince kasar Saudia ta ci gaba da kai hare hare kan manya manyan cibiyoyin rayuwan mutanen kasar Yemen da kuma kan fararen hula ba, sai ta rama ta kuma maida martani.

Dangane da wannan Umar Ma’abuni, masanin harkokin siyasar kasar Yemen ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin kasar Yemen sun sami nasarori masu muhimmanci a kan kasar Saudiya da sojojin hayarta a kudancin kasar Yemen. Sun sami iko da wurare masu muhimmanci a yankin sun kuma kora ko sun kashe sojojin saudia da sojojin hayarsu a yankin kuma suna kara ci gaba.

Ya ce, amma sojojin saudia sun maida hankali wajen ruda manya manyan ayyuka a kasar Yemen wadanda suka hada da gadoji cibiyoyin bada wuran lantarki gidajen mutane, inda suka kashe fararen hula inda sukakashe da dama daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted