Yemen: Mun Aiwatar Da Hare Hare 9 Kan Cibiyoyin Mai A Saudia

Kakakin sojojin kasar Yemen Kanar Yahyah Saree ya bada sanarwan cewa, sojojin kasar daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 19 ga watan Augusta da

Kakakin sojojin kasar Yemen Kanar Yahyah Saree ya bada sanarwan cewa, sojojin kasar daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 19 ga watan Augusta da muke ciki sun kai gungun hare hare hare kan kasar Saudia. Sun kuma hada da jiragen dakon man fetur 8 a cikin tekun red sea da wasu jiragen ruwa 3 a tekun Aden da  tekun larabawa.

Banda haka sojojin sun  tilastwa jiragen dakon mai har guda 48 komawa daga inda suka fito don tabbaka killacewa da killacewar da Saudiya take kasar ta Yemen shekaru 12 da suka gabata.

Kanar Saree ya kara da cewa, a cikin wannan lokacin sojojin Yemen sun kai hare hare da makamai masu linzamu samfurin bilistic kan cibiyoyin man fetur na gabacin kasar  Saudia, Har ilayau da cibiyoyin man Yanbu, Najran Jeejan da Abha.

Kakakin sojojin na yemen ya bayyana cewa jimilla jiragen ruwan kasar Saudian da sojojin Yemen suka kaiwa hare hare  ko suka tilasta masu komawa daga shiga mashigar ruwa ta babaul mandab 56 ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted