Shugaban hukumar leken asiri na Ecuador da Amurkawa biyar sun mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Kenya
Shugaban leken asiri na Ecuador, Michel Sensi Contougui, da matarsa ’yar Amurka, gami da wasu ‘yan Amurka hudu, da kuma matukin jirgin sun mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a kasar Kenya a ranar Laraba, a cewar hukumomin Amurka da Ecuador.
Mutane bakwai sun mutu lokacin da jirgin helikwafta da suke tafiya a ciki ya fadi a lokacin da aka bayyana shi a matsayin tafiya ta nishaɗi a yankin Samburu da ke tsakiyar Kenya.
Kafar watsa labaran ta ABC News ta ruwaito wani shugaban ‘yan sanda na yankin yana cewa matukin jirgin, wanda shi ma ya mutu a hatsarin, ɗan Kenya ne.
Shugaban hukumar leken asiri mai shekaru 44 abokin shugaban ƙasa ne na hannun dama Daniel Noboa, wanda a halin yanzu yake jagorantar ƙasar, kuma ya yi aiki a matsayin wakilinsa a kamfanonin gwamnati, musamman kamfanin mai na ƙasa, Petro Ecuador.
Sensi Contougui, wanda aka naɗa shi shugaban hukumar leken asiri a shekara ta 2014, ya yi aiki na ɗan lokaci a matsayin ministan cikin gida. Kafin ya shiga aikin gwamnati, ya kasance attajiri ɗan kasuwa a masana’antar kayan kwalliya.