Qalibaf: Kasashen Waje Basa Da Wuri A Sauye Sauyen Yammacin Asiya

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa kasashen waje basa da magana a makomar yankin yammacin Asia. Ya kuma kara da

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa kasashen waje basa da magana a makomar yankin yammacin Asia. Ya kuma kara da cewa sauye sauye masu muhimmanci suna ci gaba da faruwa a yankin, inda wadan nan manya manyan kasashen duniya basa da wuri a cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya kara da cewa Muhammad Bakir Qalobof ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Laraba, bayan shigowarsa kasar ta Iraki.

Kakakin majalisar dokoki na kasar Iran ya tsaya a wurin da shugaba Trump ya bada umurni a kashe Janar Qasim Sulaimani Shahid kwamandan dakarun rundunar Qudus na IRGC da kuma mai masaukin bakinsa Hajj Mahdi Muhandis a wajen tashar jiragen sama na Bagdaza, inda ya yi jawabi na girmama wadan nan shahidar da kuma wadanda suke tare da su.

A ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta 2020 ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurnin a kashe su. Saboda su ne suka taimakawa kasashen Iraki da siriya suka kauda ikon kungiyar yan ta’adda ta Daesh a kasashen

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted