Najeriya Ta Ajiye Naira Tiriliyin N15 Saboda Dauke Tallafi

Ministan kudade a Najeriya Taiwo Oyedele, ya bada sanarwan cewa gwamnatin Tunubu ta ajiye naira tiriloyon 15.8 tsakanin shekara 2023-2025 daga dauken tallafin da ta

Ministan kudade a Najeriya Taiwo Oyedele, ya bada sanarwan cewa gwamnatin Tunubu ta ajiye naira tiriloyon 15.8 tsakanin shekara 2023-2025 daga dauken tallafin da ta yiwa manfetur a kasar.

Jaridar daily trust ta Nageria ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba, a lokacinda yake bayyana irin ci gaban da gwamnatin shugaba Tunubu ta sami a cikin wannan lokacin.

Oyedele ya ce, gwamnatin tarayyar ta yi amfani da naira triliyin 5.4 daga cikinsu a yayinda ta rabawa jihohi da kananan hukumomi naira tiriloin 10.4.

Banda haka ministan ya kara da cewa gwamnatin tarayyar ta sami wasu karin kudade har naira triliyon 3.1 ta wasu hanyoyi. Sannan a bangaren basussuka kuma sunkai naira triliyon 11.9. Yace jimillar abinda gwamnatin tarayya ta samu a cikin wannan  lokacin ya kai naira T 20.4.

Sai dai masana da dama suna tamabaya, kan cewa menene amfanin duk wadannan kudade ga mafi yawan yan Najeriya wadanda suke cikin halin kakani kaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted