Falih Al-Fayyad shugaban dakarun Hashu Al-Shabi na kasar Iraki ya bayyana cewa Iran ta fuskanci yaki mai kama da na duniya, amma kuma ta sami nasara a cikinsa.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Al-Fayyad yana fadar haka a hirar da ta hada shi da tashar talabijan ta Ash-sharqiyya JMI ta fuskanci yaki mai kama da taduniya amma kuma ta sami nasarar tsallaka dukkan matsalolin da ta fuskanta.
Yace: HKI da Amurka sun lallata al-amuran tattalin arziki a yankin sanadiyyar yakin da suka dorawa JMI. Ya ce a cikin yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI makiya kai kai hare hare kan wuraren dakarunsa har fiye da 100 a cikin kasar iraki, daya daga cikin wuraren da suka kaiwa hari gidansa ne.
Fayyad ya kara da cewa a cikin yakin mutane kimani 100 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama sun ji rauni.
Daga karshe Fayyad ya kammala da cewa shawarar shiga ko tsaida yakin ba a hannummu yake ba, dakarun suna karban umurni daga babban kwamandan sojojin kasar Iraki ne.