Natanyahu.: Shigowar Sojojin Turkiya Siriya Barazana Ce

Shugaban kasar Amurka yar ta’adda Donal Trump ya bayyana goyon bayansa ga hare hare na baya bayan nan wadanda HKI ta kai kan tashar jiragen

Shugaban kasar Amurka yar ta’adda Donal Trump ya bayyana goyon bayansa ga hare hare na baya bayan nan wadanda HKI ta kai kan tashar jiragen sama na Abu-Azzuhur da ke wajen birnin Idlib na arewacin kasar Siriya, ya kuma kara jadda goyon bayansa ga mamayar da HKI take wa yankuna da dama na kasar Siriya daga ciki har da tuddan Golan na kudancin kasar.

Shugaban kasa yar t’adda ta Amurka a zantawar da tashar talabijan ta Chennel 12 ta HKI ya ce ya san dalla dalla yanda hare haren suka kasance amma ya zabi yin shuru a halin yanzu.

A wani labarin kuma Benyamin Natanyahu firay ministan HKI ya bayyana cewa, haramtacciyar kasarsa ba zata taba amincewa gwamnatin kasar Turkiyya ta samar da sansanin sojoji a cikin kasar Siriya ba.

Ya kuma kara da cewa sojojin kasar Turkiyya a cikin kasar Siriya barazana ne ga tsaron haramtacciyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted