Majiyar hukumar Agaji a yankin Gaza ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahadai a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata sun kai 17.
A cikin birnin Gaza, majiyar ‘yan sanda ta bayyana cewa; harin sojojin sahayoniyar an kai shi ne akan wani ofishin ‘yan sanda wanda ya yi sanadiyar shahadar 9 daga cikinsu da kuma jikatar wasu da dama.
Majiyar ta kuma ce, ‘yan mamayar sun yi wa mutane kisan kiyashi mai tsanani akan ‘yan sanda.
A wani labarin na daban, majiyar Asibitin “Audah” ta ce wani Bafalasdine guda daya ya yi shahada a sanadiyyar wani hari na sojojin Isra’ila a kan mahayin wani babur a sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” a tsakiyar Gaza.
Ita kuwa ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a jiya Talata cewa mutane 7 ne su ka yi shahada daga cikinsu har da karamin yaro da kuma jikkatar wasu da dama.
Bayan harin da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai wa gabar Ruwan Gaza, kungiyar Hamas ta bayyana cewa; Abinda Benjamine Netanyahu yake yi, shi ne kokarin rusa tattaunawar da ake yi, da kuma keta yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kungiyar ta Hamas ta ce a nata bangaren tana kokarin ganin an cimma nasarar yarjejeniyar, tare da yin kira ga Amurka da sauran masu shiga Tsakani da su tilastawa “Isra’ila” aiwatar da yarjejeniyar.
Hari da sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai a gabar Ruwan Gaza ya yi sanadiyyar shashadar wani adadi mai yaw ana fararen hula da kuma jikkata wasu.