Somaliya:Mutane Da Dama Sun Kwanta Dama A Fadan Kwance Iko Da Baidoa

 Fada mai tsanani ya barke a tsakanin sojojin gwamnatin Somaliya da kuma masu adawa da ita a kokarin kwace iko da garin Baidoa mai muhimmanci

Sojoji A Garin Baidoa

 Fada mai tsanani ya barke a tsakanin sojojin gwamnatin Somaliya da kuma masu adawa da ita a kokarin kwace iko da garin Baidoa mai muhimmanci dake yankin kudu masu yammacin kasar.

Rahotannin da suke fitowa daga yankin sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu daga cikinsu da akwai fararen hula hudu.

A ranar Litinin din da ta shude ne fadan ya barke a tsakanin sojojin na gwamnati da kuma masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Abdulaziz Hassan Muhammad bayan da su ka kai hare-hare a kan wasu cibiyoyi na gwamnati.

Gwamnatin tarayyar kasar ta Somaliya ta tabbatar da cewa da akwai ‘yan kungiyar “alshaba” da suke fada a tare da mayakan masu goyon bayan tsohon shugaban kasar.

Ministan harkokin cikin gida Isak Muhammad Korsaar ne ya tabbatar da hakan sannan kuma ya kara da cewa: Sun kama wasu daga cikin mayakan al-shabab a lokacin fadan na garin Baidoa.

Sai dai a jiya Talata yakin ya dan lafa, kuma sojoji sun fara sintiri akan manyan hanyoyin garin da kuma duba motocin da suke kai da komawa.

Mazauna birnin suna kaucewa ficewa daga cikin gidajensu, duk da cewa da akwai  sojoji masu yawa akan tituna.

Majiyar Asibiti ta ce akalla mutane 100 ne su ka jikkata.

Da akwai mutane da yawansu ya kai dubu dari biyar da yaki ya koro su daga yankunasu, wadanda suke rayuwa a cikin wannan garin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted