221-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu dawarhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissashi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu laiattafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…. Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da mukekawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka fara magana kan Hijru dan Adi sahabin manzon All..(s) kuma daya daga cikin fitattun shi’ar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma dansa Imam Al-Hassan(a) mutumin kufa kuma shugaba daga cikin kabilar Kinda. Yayi fice da tsoron All..(ST). mai yawan ibada, mutum ne wanda All..yake karban addu’arsa.
Mun bayyana yansa wanka janaba ta kama shi a kan hanyar zuwa sham , amma mai kula da shi yaki ya bashi ruwa, sai ya daga hannayensa ya roki All..ya yi masa hanyar raba kansa da dauda, sai ba’a dade ba aka yi ruwansama sai ya samu yayi wanka.
Kafin haka mun bayyana yanda yake tsayawa a gaban ma’aikatan Mu’awiya a Kufa, Mughira dan shuaba, da Ziyad dan Sumayya, saboda sabon All.. da suka aikatawa.
Mun bayyana yanda Ziyar yayi khudubar sallar Jumma’a har sai sura lokaci kadan lokacin sallah ya fita, Hijru ya jagoranci mutane suka tilasta masa yanke huduba da kuma sallah kafin lokacinta ya fice. Kuma wannan shi ne farkon abinda ya fara hada shi da Ziyad dan Sumayya. Daga nan ya nemi ya kama shi ya kasa sai da ya hada da manya manyan mutanen kufa wadanda suka hada da Mohammad dan Ash’as Alkindi suka taimaka masa suka kama shi da magoya bayansa aka jefasu a gidan yari.
Sannan suka kirkiro shaida ta kariya tare da taimakon Abu burdata dan Abu Musa Al-ash’ari wanda ya rubutata, mutane 70 suka sanya hannu a kanta. A lokacinda Mu’awiya ya karbi wasikar ya karantata ya kuma ga sunayen mutanen kufa kimani 70 wadanda suka amince da ita, sai ya bada umurnin a zo da shi da wadanda suke tare da shi kasar sham, a cikin sarkoki.
Ziyad ya bada umurni a fito da su don tafiya kasar sham a cikin dare, a lokacinda ayarin ta kama hanyar tafiya sai diyars, wacce ita ce kadai ya bari a bayan ta hau kan rufin gidansu tana masa kallo da bankwana na karshe tana kuka tana rera wasu kasidu wadanda suke bayyana bakin cikinta dangane ta fiyar mahaifinta zuwa sham tafiyanda babu dawowa.
A lokacin da ayarin Hijru dan Adi ya isa wani wuri da ake kira Murji Azraa, dake wajen birnin Damesh sai Hijru ya ce, wallahi nine musulmi na farko da ya wanda karnukan wannan garin suka yiwa haushi, kuma nine musulmi na farko wanda ya yi kabbara a cikinsa).
Sai suka aiki dan sako zuwa wajen Mu’awiya don sanin inda za’a kaisu, ko abinda za’a yi da su. A lokacinda dan sako ya dawo, sai suka ga dan sakon wani mutum ne wanda idonsa guda ya makance.
Sai wani daga cikinsu ya fadawa sauran, idan kamar yadda nake ganin wannan dan sakon gaskiya ne, to za’a kashe rabimmu sauran kuma zasu tsira. Sai suka tambaye shi, ta yaya? Sai yace: baku ga cewa dan sakon yana da ido daya ba?.
Dan sakon mu’awiya ya isar da sakon cewa, a kasashe gaba daya, sai idan sun zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) sun kuma baranta kansu daga gareshi.
Ba’a jima ba sai shugaban ma’aikatan mu’awiya ya zo wajen Hijru ya fada masa cewa, Ya kai shugaban batattu, kuma ma’ajiyar kafirci, da dagawa, kuma mabiyan Abuturab, amirulmuminina yace a kashe ka, sannan in kashe mutanenka idan sun ki tuba daga kafircinsu, sun la’ani mutuminku sun kuma barranta daga garesu.
Daga nan sai gaba daya suka fada da murya guda, suna bayyana imaninsu, da cewa: Lalle hakuri da kaifin mashi ya fi mana sauki daga abinda kuke kirammu zuwa gareshi. Sannan komawa ga All..ga kuma manzonsa (a) da kuma wasiyyas ya fiye mana daga shiga wuta.
Daga nan sai rabinsu suka amince suka yi aminda mu’awiya ya ce su yi, sauran kuma suka tabbata kan amaninsu na bin Amirulmuminina (a) .
Don haka sai aka gina rami ko kaburbura ga wadanda suka ci gaba da rike imaninsu suka ki amince was u zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) daya bayan daya suka kashe suka sasu a kabubrburansu.
A lokacinda suka zo kan Hijru sai ya bukacesu su bashi wata dama kafin su zartar da hukuncin kasa a kans, ku barni in yi alwala inyi salla? Ban tana alwala bas ai na yi salla.
Sai suka amince masa ya yi alwala ya kuma yi salla, ya dan tsawita sallarsa, a lokacinda ya kammala sai ya ce masu, wallahi ban taba salla mai sauki irinta ba, in badon kada ku yi zaton ina tsoron mutuwa ne da tsawaitata.
Daga nan sai Hijru y afara munajati da Ubangijinsa yana kuka masa yanda mutanensa suka mikashi ga makiyansa, yana cewa: Ya Ubangiji, muna neman tsarinka daga al-ummarmu, lalle mutanen kufa sun yi shaida a kammu, kuma gashi mutanen sham zasu kashe mu, kuma wallah idan kun kashemi a cikinta, to na rantse da All…nine musulmi na farko mayaki da ya ce la’ilaha illah a cikinta, . Kuma nine musulmi na farko da karnukan ta suka yi masa haushi.
Daga nan sai Hadabah dan Fayyad Alkadaaiy a matso kusa da shi, da takobinsa a zare, a lokacinda Hijiru ya ganshi sai ya sai jikinsa yayi karkarwa, sai suka ce masa , amma kana riya cewa, baka tsoron mutuwa ba, ka baranta daga mutuminka mu barka.
Sai Hijir yace masu: Me yasa ba zai firgice ba? Iana ganin an haka kabari? Ga likkafani a warwareshi, ga kuma takobi an zareshi. Kuma ko da kunga na kadu daga mutuwa amma ba zan fadi abinda zai fusta Ubangiji ba. Kalma ta karshe da ya fito daga bakinsa it ace: kada ko kwancike karafuna da aka dabaibayeni da su, kada ku wanke jinin da ya zuba daga gareni, lalle zan hadu da mu’awiya kan da gaske.
A cikin wannan halin jikin Hiji rya fadi kasa, a jike da jininsa, tareda sauran mutane 6 da suka zama shahidan Akida na farko a tarihin addinin musulunci. Sun zama abin buka misali har duniya ta nade na riko da ikida.
Wannan ya nuna cewa su 7 ne, wadanda suka jada baya daga cikinsu kuma 7 ne don haka Hijru da mutanensa su 14.ne.
Suwaye sahabban Hijir guda 6 wadanda suka yi shahada tare da shi? Suka rubuta sunayensu da jininsu ta yanda tarihi ba zata manta da su ba?.
Ga sunayen sahabban Hijir wadanda suka saida ransu don tsira da ikadarsu , har zuwa ranta za’a tacesu da wannan akidar tasu. Ranar da azzlumai zasu gane cewa wanda suka yi Imani da shi shine mai ranar, shine abin girmamawa a wajen All… sun hada da.
01-Abdurrahman dan Hassan Al-Anzi, a lokacinda ma’aikatan Mu’awiya suka zo zasu kashe shi sai ya ce masu, su kaishi wajen Mu’awiya mai yuwa za iyi amfawa gareshi. Sai suka amince suka kai shi gaban Mu\awiya. Sai Mu’awiya yace masa:
Ya kai mutumin kabilar Rabii, me zaka fada dangan Ali(a). sai yace ka barni kada ka tambaye wannan don ya fiye maka alkhairi.
Sai Mu\awiya yace wallahi ba zan barka ba. Sai Abdurrahman yace: Na shaida yana daga cikin masu ambaton All..da yawa, mai umurni da gaskiya, kuma yana daga cikin masu tsaida adalci, mai kuma yin afwa ga mutane.
A nan mu’awiya bai sami abinda zai sa ya halatta zubar da jininsa ba. Sai ya koma kan jinin Uthman wannan All..ya jarraba musulmi da jininsa a raye da kuma bayan mutuwarsa. Sai yace masa. Me zaka ce dangane da Uthman .
Sai Abdurrahaman ya ce, shi ne na farko da ya bude kofar zalunci ya kuma rufe kofar gaskiya. . sai mu’awiya yace: Ka kashe kanka. Sai yace : kanka ka kashe.
Daga nan sai Mu’awiya ya ce a dauke shi daga gabansa. Sannan ya rubuta wasika zuwa walinsa a Kufa Ziyad dan Sumayya inda a cikinta ya fada masa cewa wannan dan kabilar Al-Anzi shi ne mafi munin wadanda ka aiko mani, ka kashe shi mafi sharrin kisa. A lokacinda wasikar ta isa hannun Ziyad sai ya turashi wani wuri a wajen Kufa wanda ake kira ‘Kassun Natiki’ aka binne shi da ransa ha rya mutu.
02-sai kuma Saifi dan Fasil alshaibaniwanda ya kasance daga cikin jaruman musulmi, kuma masu yawan ilminsu, da kuma fitattun daga cikinsu, ya kasance cikin zababbun mutanen Hijru.
Da farko tun a kufa, an kaiwa ibn Ziyad labarinsa kan cewa masoyoyin Aliyu dan Abitalib(a) ne. Sai Ziyad ya aika masa, sai ya zo, sai ya fara tambayarsa dangane da Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a)
Ya ce: Ya makiyin All..me zaka fada dangane da Abuturab, sai ya amsa: ban san Abu turab ba. Sai yace: Ka sanshi kuwa: ya ce: Ban sanshi ba, sai Yace: Bakasan Aliyu dan Abitalib (a) ba?. sai yace: ee na san shi. Sai yace: Shi ne Abuturab.
Sai ya ce: Ba haka ba, shi ne baban Alhssan da Alhussin (a). sai shugaban yansanda ya ce masa: Amir yace maka shi ne Abuturab kashe ba haka ba.?
Sai saifi ya ce masa: Idan Amir ya yi karya, kanason ni ma in yi karya. In shaida masa kan karyan da ya fada?. Sai ziyad yayi fushi ya ce: wannan kari a kan laifukanka.
Sai na biyunsu. 367