Pezeshkian: Ra’ayin Kasashen Turai Kan Iran Kuskure Ne

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ra’ayin ƙasashen Turai game da Iran bai yi daidai da gaskiya ba Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ra’ayin ƙasashen Turai game da Iran bai yi daidai da gaskiya ba

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana cewa: Fahimtar da wasu ƙasashen Turai ke yi game da Iran ba daidai ba ne kuma ba ta nuna gaskiyar ƙasar.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Shugaba Mas’oud Pezeshkian ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin wani biki na karɓar takardar shaidar Mr. Christian Atsen, sabon jakadan Denmark a Iran. Yana mai jaddada yanayin mutanen Iran masu son zaman lafiya da buɗe ido, ya ce: “A tsawon tarihi, mutanen Iran sun kasance masu son zaman lafiya, suna ƙoƙarin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma mu’amala mai kyau da sauran ƙasashe. Denmark tana cikin ƙasashen da Iran ke neman faɗaɗa dangantaka da haɗin gwiwa da ita.”

Da yake magana game da wasu ra’ayoyi da wasu mahanga da suka mamaye Turai game da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Shugaban Pezeshkian ya jaddada cewa: “Tunanin da wasu ƙasashen Turai suke dauke da shi game da Iran ba daidai ba ne kuma bai dace da gaskiyar da ke ƙasa ba. Pezeshkian ya kara da cewa: Yana da tabbacin cewa: A lokacin da tawagar suke cikin Iran, za su iya lura da gaskiyar al’ummar Iran, al’adu, da wayewarsu, kuma hakan zai iya taka rawa wajen gyara wannan fahimta ta kuskure da kuma isar da hoton Iran mai inganci da gaskiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted