Janar Sari: Fiye Da Sojojin Saudiyya Da ‘Yan Korenta  200  Aka Kashe Da Kuma Jikkatawa A Cikin Sa’o’i Kadan

Gwamnatin Yemen ta sanar da cewa  ta kashe tare da jikkata sojojin Saudiyya da ‘yan korenta 200 a yankin Ra’asul-al-arah wal saqyah, haka nan kuma

janar yahya sari

Gwamnatin Yemen ta sanar da cewa  ta kashe tare da jikkata sojojin Saudiyya da ‘yan korenta 200 a yankin Ra’asul-al-arah wal saqyah, haka nan kuma ta kai wasu jerin hare-haren  a gabashin Jauf da gabashin Raqwan a gundumar Ma’arib.

Kakakin sojan Yemen janar Yahya Sari ne  ya yi wannan sanarwar sannan ya kara da cewa; Bayan sojojin da su ka kashe da kuma jikkatawa sun kuma kone motocin yaki da dama.

Haka nan kuma ya ce; za su ci gaba da kai wa sojojin saudiyya da na ‘yan korenta hare-hare ba tare da kakkautawa ba.

Kakakin sojan gwamantin Sanaa ya kuma yi watsi da ikirarin ‘yan koren Saudiyya na cewa sun shiga wasu yankuna na gundumar Ta’iz, tare da cewa abinda suke fada kurari ne da kokarin nuna jarunta ta fatar baki da babu ita a kasa.

 A gefe daya tashar talabijin din “Almayadin” ta nakalto wani kwararre a fagen soja na kasar ta Yemen janar Abdulgani al-Zubaidi yana fadin cewa; ‘yan koren Saudiyya da su ka yi kokarin kutse cikin yankin ‘al-makha’ sun ranci na kare bayan da aka fatattake su.

Janar Zubaidi ya kara da cewa; masu samun goyon bayan Saudiyyar sun yi kokarin shiga yankin amma sun sha kashi bayan da dakarun Yamen su ka kora su.

A wani labarin mai alaka da Yemen, a jiya da marece Saudiyya da Turkiya da Pakistan sun sanar da kafa rundunar hadin gwiwa domin kare kasar ta Saudiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted