Ministan Harkokin Cikin Gidan Iran Ya Isa Birnin Doha Na Kasar Qatar

Ministan harkokin cikin gidan Iran Askadar Mumini ya isa birnin Doha na kasar Katar  tare da samun kyakkyawar tarbar karamin ministan harkokin cikin gidan kasar

mumini a birnin Doha

Ministan harkokin cikin gidan Iran Askadar Mumini ya isa birnin Doha na kasar Katar  tare da samun kyakkyawar tarbar karamin ministan harkokin cikin gidan kasar Abdulaziz Bin Faysal.

Ma’aikatar harkokin  cikin gidan Iran ta sanar da cewa; A yayin wannan ziyarar Mumini zai tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashen biyu, bayan da ya amsa gayyatar takwaransa na Qatar Khalifa Bin Hamad Bin Khalifa ali-Thani.

Daga cikin manufofin ziyarar da akwai musayar bayanai da aiki tare a fagen fada da ta’addanci da kuma tsararrun laifuka da fasakwaurin muggan kwayoyi. Haka nan kuma tattaunawar za ta shafi tabbatar da tsaro a iyakokin kasar na ruwa da tsaro ta fusakar hanyoyin sadarwa na Internet da kuma aiki tare a tsakanin ‘yan sanda.

Sanarwar ta kuma ce bangarorin biyu za kuma su yi musayar ra’ayi akan abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin da aiki tare a fagen musayar dalibai da aiki a tsakanin jami’o’in kasar.

 Da akwai kwararru da dama a cikin tawagar ta ministan harkokin cikin gida zuwa Qatar da su ka hada Mahdi Dusti, mataimakin minista akan harkokin tattalin arziki da raya kasa, da kuma Mahdi Musawi mai bai wa ministan shawara, da wasu da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted