Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Mutne Fiye Da Goma A Yemen

Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai wasu munanan hare-hare kan kasar Yemen tare da kashe mutane fiye da goma Rahotonni sun watsa labarin cewa: Jiragen

Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai wasu munanan hare-hare kan kasar Yemen tare da kashe mutane fiye da goma

Rahotonni sun watsa labarin cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare ta sama masu tsanani a yankuna daban-daban na Yemen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Yemen 13 da kuma jikkata wasu na daban.

Kamfanin dillancin labaran Mehr, wanda ya nakalto daga kafar Al-Masirah na Yemen ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare kan yankunan Ali al-Amri da Bab al-Mandab a Dhubab sau shida, da kuma yankin Haifan sau uku.

Gundumar Sa’ada, a arewacin Yemen, hare-haren jiragen saman Saudiyya sun kwashe ‘yan mintuna suna luguden wuta kan gidajen jama’a.

A halin yanzu, wakilin gidan talabijin na Al-Mayadeen a Yemen ya ruwaito cewa: Bayan hare-haren jiragen saman Saudiyya a kan iyakokin yankunan Sa’ada da Hajjah, mutane bakwai sun mutu wasu shida kuma sun jikkata.

Saudiyya ta kuma kai hari kan gonaki da gidaje a garuruwan Sahar da Saqin a lardin Sa’ada da makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted