Mataimakin shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Ali Nikzad ya bayyana cewa; Sake bude mashigar Ruwan Hurmuz da bude shi ne suke ayyana farashin makamashi a kasar Amurka, ba sakwanni marasa ma’ana da shugaban kasar Amurka yake wallafawa a shafukan sada zumunta ba.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto mataimakin shugaban majalisar shawarar musuluncin na Iran yana cewa; ba zama abin mamaki ba da kasa mai karfi ta koma aiki da parpaganda bayan da ta sha kashi a hannun al’ummar Iran, ta kuma rika kwakwazo, sai dai a fili yake cewa, filin daga ne yake ayyana makomar da aka dosa ba surutu ba.””
Haka nan kuma ya ci gaba da cewa; Abinda Amurkan ta so yi, shi ne mayar da Iraki wani bangare nata, amma a karshe ta fice daga cikin kasar a cikin kaskanci bayan da ta yi asarar dubban rayuka da jikkatar wasu dubban.”
Bugu da kari mataimakin shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; barazana da kurararin da shugaban kasar Amurka yake yi, saboda samun karbuwa ne a cikin gida da kuma yin tasiri a cikin zabukan kasar masu zuba, don haka maslahar Amurka ita ce ta rusuna a gaban manufofin al’ummar Iran.