A wani labari da jaridar “Daily Trust” ta Nigeria ta buga ta ambaci cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an tsaron na Nigeria su ka kashe Aka Anwar wanda kwamanda ne na kungiyar nan ta ” ISWAP” a yayin wani farmaki da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata.
Kakakin soja Innocent Olamale na rundunar sojoji ta 32 a garin Akure ya tabbatar da kai hari yana mai kara da cewa; An kashe dan ta’addar ne a tare da wasu mambobin kungiyar.
Haka nan kuma ya ce; Hari ne aka kai na hadin gwiwa wanda ya kai ga kashe kwamandan kungiyar “Daular Musulunci A Yammcin Afirka ( ISWAP) a takaice.”
Manjo Olamale shi ne mataimakin darakta na bangaren tuntubar jama’a a rundunar ta sojoji.
An kai farmakin ne bayan da aka sami bayanai na sirri akan cewa kungiyar ta masu tada kayar baya suna Shirin kai wasu hare-hare.
Majiyar sojan na Nigeria ta kuma ce; Sun sami bayanan sirrin ne daga cikin gida da kuma abokan aikinsu na kasashen waje akan makarkashiryar da kungiyar ta ISWAP take kitsawa.
Wanda aka kama din yana da hannu a wani hari da akai taba kai wa a ranar 31 ga watan Disamba a 2025 a kan ofishin ‘yan sanda na Ipele a garin Owo tare da sace bindigogin Ak-47 guda takwas. Haka nan kuma an kone ofishin ‘yan sandan ta hanar tashin bama-bamai.
Haka nan kuma yana da hannu a wani harin na ranar 28 ga watan Yuli 2022 akan wajen binciken sojoji akan hanyar Suleja-zuba a Jahar Niger, da kuma wani harin na ranar 11 ga watan Yuli 2022 a kan gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.