Wadanda Suka Bace A Ambaliyar Ruwan Nepal Sun Kai 2,400

Yawan mutanen da suka bace a ambaliyar ruwa mai kama da Tsunami a kasar Nepal da China sun fi 2400, kamar yanda hukumomin ceto da

Yawan mutanen da suka bace a ambaliyar ruwa mai kama da Tsunami a kasar Nepal da China sun fi 2400, kamar yanda hukumomin ceto da bada agajin gaggawa suna sanar.

Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto hukomomin kasar Nepal na cewa daga cikin wadanda har yanzun ba’a da labarinsu akwai yan kasashen waje kimani 517. Sannan sauran kuma yan kasashen biyu ne.

Ya zuwa safiyar yau Asabar, labarai daga kasar Nepal sun bayyana cewa ma’aikatan ceto NUWAKOT na kasashen China da Nepal suna aiki don zakulo ko gano wadanda suke da sauran shan ruwa daga burbushin ambaliyar ruwan na ranar 26 ga watan Augusta.

A jiya dai an bada labarin cewa wadanda har yanzun ba’a san makomarsu ba ya kai 2,400 sannan an zakulo gawakin mutane 586. Kafafen yada labarai na kasar sun bada sanarwan cewa ambaliyan ruwan ya share kome a kan hanyarta har zuwa zuwa cikin kasar Indiya.

Hukumar bada agaji na Nepal ya bada sanarwan cewa, ma’aikatan madatsan ruwa na bada wutan lantarki 933 da wasu masu tattalin ziyarar addinin a duwatsun Kailash a Tibet duk suna daga cikin wadanda ba’a sake jin duriyarsu ba.

Dukkan matsugunan mutane kusa da kogin ruwan ambaliyar ta sharesu gaba daya. Inji kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa.

Kungiyar bada agaji ta duniya Red Croos ta bayyana cewa mai yuwa wadanda abin ya shafa zai kai mutane 93,000 a dai dai lokacinda ake ci gaba da gano gawakin mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted