Syria: Sojojin Isra’ila Sun Kutsa Cikin Kasar Fiye Da 1000 Tun Faduwar Gwamnatin Basshar Asad

Syria: Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Kasar Fiye Da 1000 Tun Faduwar Gwamnatin Basshar Asad
taswirar Syria

 Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Syria “almirsad” ta sanar da cewa; Daga faduwar gwamnatin Basshar Asad  a watan Disamba zuwa yanzu sojojin Hamratacciyar Kasar Isra’ila sun kutsa cikin kasar sau 1004.

Sanarwar ta kuma ce baya ga kusten da sojojin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka yi a cikin Syria din sun kuma kame mutane da kuma kartar kasa da lalata hanyoyi da gonani da kafa cibiyoyin bincike na soja. Haka nan kuma jiragensu na yaki sun rika yin shawagi a samaniyar kudancin kasar ta Syria.

Bayanin ya kuma ce a cikin shekarar 2025 da ta gabata, sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan sun shiga cikin Syria har sau 460,to amma da aka shiga wannan shekara ta 2026 yawan shigar tasu ya karu inda ya kai 530 har zuwa watan Ogusta. 

A makon  farkon faduwar gwamnatin Basshar Asad kuwa a Disamba na 2024  sojojin mamayar Haramtacciyar kasar Isra’ilan sun shiga cikin kasar sau 14.

Bugu da kari sojojin mamayar na Haramtacciyar Kasar sun rika kama fararen hula da kuma bincike masu kai da komawa a yankunan da suke kutsawar. Sai kuma kartar kasa domin kafa wuraren zaman soja da gudanar da bincike na masu kai da komawa.

A can yankin Qunaidhara ma sojojin mamayar na Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna shiga kusan a kowace rana, haka nan kuma a yankin Dar’a da suka kafa wuraren bincike da shiga cikin gidajen mutanen yankin.

A makon da wuce ministan tsaron “Isra’ila” Kats ta tsaya akan “Jabalush-sheik mai nisan kilo mita 35  daga birnin Damascuss ya gargadi shugaban kasar Syria Ahamd Shar’da cewa; Idan ya daga kansa da safe zai hango Isra’ila tana wannan wurin domin kare kanta.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted