Falasdinawa biyar ne suka yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun safiyar Asabar
Falasdinawa biyar ne suka yi shahada yayin da wasu goma suka samu raunuka a ranar Asabar a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza tun daga safiyar ranar Asabar.
Waɗannan hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ke aiki a Zirin Gaza tun daga ranar 10 ga Oktoban shekara ta 2015.
Majiyoyin lafiya a Gaza sun ruwaito cewa: Falasdinawa uku sun yi shahada ne yayin da wasu shida suka jikkata a hare-haren jirginn saman yakin sojojin mamayar Isra’ila da suka kai kan garin Khan Younis da Birnin Gaza, yayin da wasu uku suka jikkata a wani harin bam da ya kai wani ma’ajiyar magunguna a cikin Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al-Balah a tsakiyar Zirin Gaza.