Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hare-hare da jiragen yaki a yankuna mabanbanta na kudancin Lebanon da su ka hada da Tuddan Ali Tahir da Nabadhiyya da kuma yankin Maslakh.
Jiragen yakin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hare-haren ne da marecen yau Asabar a yankin na “Ali Tahir” a arewacin Nabadhiyya.
Sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila dai ba su aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Lebanon.