Iran: Jami’an Tsaro Sun Kara Da Yan Ta’adda A Saravan

Jami’an tsaro na JMI sun bada labarin wargaza wani shirin hare hare kan garin Saravan da ke yankin siatan Baluchestan daga kudu masu gabacin kasar

Jami’an tsaro na JMI sun bada labarin wargaza wani shirin hare hare kan garin Saravan da ke yankin siatan Baluchestan daga kudu masu gabacin kasar a jiya da dare.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na JMI ya bada labarin cewa hadin giwa tsakanin dakarun IRGC ne da na leken asiri suka gano inda yan ta’addan suke suna kuma fafata da su sanan suka kashe wasu daga cikins.

Sun kuma kwace makamai da dama daga hannunsu.

Makaman sun hada da AK 47 RPG-7 da boma bomai. Wadanda suka shiga hannu daga cikinsu, suna da hannu wajen kashe jami’an tsaron kasar Musamman IRGC a bayan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted