Ibn Riza: Wajibi Ne Iran Ta Kara Karfi A Kowace Rana

Kwamandan soja  kuma mukaddashin ma’aikatar tsaron Iran Majid Ibn Riza ya bayyana cewa; Wajibi ga kasar Iran ta rika kara karfinta a kowace rana. Ibn

Ibn riza

Kwamandan soja  kuma mukaddashin ma’aikatar tsaron Iran Majid Ibn Riza ya bayyana cewa; Wajibi ga kasar Iran ta rika kara karfinta a kowace rana.

Ibn Riza wanda yake Magana akan jawabin bayan nan na jagoran juyin musulunci ya bayyana cewa; “yayanka da suke aiki a ma’aikatar tsaro, suna ci gaba da aiki da umarninku kuma suna kara karfin Iran, da kare tsaron al’umma domin takawa abokan gaba birki da haka su aikata kowane irin kuskure.

Haka nan kuma ya kara da cewa; Kallafaffen yakin karshe ya tabbatar da cewa; Iran tana da karfi, kuma wajibi ne a kowane lokacin Iran din ta kara karfin da take da shi,ya zama tana cikin Shirin fuskantar kowace irin barazana ta yau da kuma ta nan gaba.

Ibn Riza ya kuma ce; samari da matasan Iran sune abin dogarar kasar domin sune su ka yi wa Iran kere-kere a lokaci mafi tsanani,wadanda kuma da kayan da su ka kere ne aka yi aiki da su a filin yaki.

Har ila yau, Ibn Riza ya yi Ishara da yadda wanda ya assasa juyin musulunci na Iran Imam Khumaini da jagoran juyi shahidi “Ayatullah Sayyid Ali Khamnei su ka bai wa samari da matasa muhimmanci domin gina ci gaban Iran mai karfi.

Wani sashe na bayanin mukaddashin ma’aikatar tsaron Iran ya bayyana cewa; hadin kan da ake da shi a  tsakanin al’ummar Iran, a tsakanin al’umma mutanen gari da sojoji a karkashin jagorancin malami Babbar ni’ima ce wanda hakan yake a matsayin Babbar kariya ga Iran a gaban makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted